Thursday, December 26
Shadow

Ƴansanda sun gurfanar da masu zanga-zanga kan cin amanar ƙasa a jihar Borno

Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Borno ta gurfanar da mutum 19 da suka haɗa da wasu ƙananan yara uku a gaban kotu bisa zargin hannunsu a zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta.

An gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a Aisha Mohammed Ali a babbar kotun jihar da ke birnin Maiduguri a yau Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake matsa wa gwamnatin tarayya lamba kan ta janye tuhumar da ake yi wa ƙananan yara da aka kama saboda gudanar da zanga-zangar.

A cewar takardar da aka gabatar a kotun, yaran uku suna tsakanin shekaru 14 zuwa 17.

Karanta Wannan  Akwai yiyuwar a fada wahalar Man fetur saboda NNPCL tace bashi ya mata yawa

Gwamnatin jihar Borno ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da cin amanar ƙasa, da kuma amfani da kafafen sada zumunta wajen ɓata sunan gwamnan jihar, da kuma tunzura jama’a a su yi wa gwamnati karan-tsaye.

A cewar masu gabatar da ƙara, yaran suna daga cikin mutum bakwai da suka haɗa baki wajen kafa wata ƙungiya mai suna “Zanga-zanga” ta dandalin sada zumunta na WhatsApp da Tiktok, inda ake zargin sun amince da ɗaukar makamai, wanda ya saɓa wa sashe na 79 na dokar jihar Borno ta 2023.

Kazalika, an tuhumi wasu mutane 11 da laifin ɗaga tutar Rasha a bainar jama’a, amma sun musanta zarge-zargen.

Karanta Wannan  Sojan Najeriya ya dirkawa kanshi biinndiigaa ya muutuu

Mai shari’ar ta dage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba, inda ta bayar da umarnin kai yaran wuraren tsare yara masu laifi, yayin da za a ci gaba da tsare manyan cikinsu a gidan yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *