Wednesday, January 15
Shadow

Ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa ranar sallah a ƙauyen Dudun Doki na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar Sokoto

ANA BIKIN SALLAH YAN BINDIGA SUN TAFKA MUMMUNAN BARNA A SOKOTO.


Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto, inda suka kashe kuma suka sace mutane da dama da sanyin safiyar Lahadi

Maharan sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar, suka kashe mutane sama da goma, kamar yadda aka ruwaito

An ruwaito cewa, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamarin ba.

Allah ta’ala yakawo mana zaman lafiya alfarmar Al-qur’ani.

Karanta Wannan  Goron Sallah: Gwamnan Sokoto ya bai wa ma'aikatan jihar naira 30,000

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *