Friday, December 5
Shadow

Ƴansanda a Kano sun kama mutane 9 bayan rykycyn

Ƴansanda a Kano sun kama mutane 9 bayan rikicin da ya faru kan zargin kisan kai a Garko.

Rundunar ’Yansanda ta Jihar Kano ta ce ta kama mutane tara da ake zargi da hannu a tashin hankali da ya faru a karamar hukumar Garko bayan wani lamari na kisan kai.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Satumba, 2025, lokacin da jami’an ‘yansandan, shiyyar Wudil su ka kama wasu mutane uku da ake zargi da kisan kai, sannan aka kai su caji-ofis na Garko domin bincike.

Sai dai a ranar 5 ga Satumba, jama’a dauke da sanduna da duwatsu suka farmaki ofishin, suna zanga-zangar mutuwar wanda aka kashe, tare da kokarin kashe wadanda ake tsare da su.

Karanta Wannan  Ji yanda wani Mahaukaci ya kwace Bndighar Soja ya Shekye sojan a Legas

Harin ya jawo konewar motar sintirin ’yansanda, lalata motoci uku na Hisbah da na karamar hukumar Garko, da kuma lalata tagogin ginin ofishin ’yansanda.

Jami’an ’yan sanda guda uku sun jikkata, inda aka garzaya da su asibitin Wudil kuma suna samun sauki.

A lokacin hargitsin, wata tayar da aka kunna ta fashe ta bugi wani daga cikin masu tada zaune tsaye, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa, yayin da wasu uku suka jikkata.

Kwamishinan ’Yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gaggauta tura jami’ai tare da shiga tattaunawa da shugabannin al’umma, abin da ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya da natsuwa a yankin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Daya daga cikin masu Addu'a a Coci ta Sùmà ana tsaka da addu'ar, anata dai cewa wai holy spirit ne ya shigeta

Rundunar ta gargadi jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, saboda hakan na iya haifar da tada hankalin jama’a da karya doka.

CP Bakori ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da adalci. Ya kuma bukaci jama’a su kasance cikin natsuwa, su ci gaba da hadin kai da jami’an tsaro, tare da gujewa duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya.

Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin cafke sauran da ake zargi da hannu a wannan hari.