Ƴansanda biyu sun jikkata yayin artabu da ƴandaba a Kano.

Ƴansanda biyu, Abdullahi Ibrahim da Yahaya Saidu, sun samu raunuka yayin wani kazamin fada da wasu gungun ‘yan fashi da makami a jihar Kano.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar wa manema labarai a Kano a jiya Laraba.
“Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta amsa kiran gaggawa a ranar 22 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1 na rana dangane da wani gungun ‘yandaba da ake zargi Halifa Baba-Beru daga unguwar Gwammaja, karamar hukumar Dala, ya na jagoranta.
“An rawaito cewa gungun yandaban na dauke da muggan makamai kuma su ka rika kai hari kan al’umma a unguwar Gwammaja, Dala LGA, Kano.
“Lokacin da ‘yansanda suka isa wurin, sai yandaban su ka yi tirjiya har da kai wa ƴansandan hari, wanda ya janyo fafatawa mai zafi. Jami’ai biyu, Abdullahi Ibrahim da Yahaya Saidu, sun samu raunuka,” in ji Kiyawa.
Ya kara da cewa jagoran yandaban, Baba-Beru, shi ma ya samu mummunan raunuka a jikin sa inda dukkan wadanda suka jikkata aka garzaya da su zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano.
A cewar Kiyawa, Baba-Beru ya rasu a asibiti yayin da yake karbar magani, yayin da jami’an ‘yansandan da suka jikkata suka warke kuma aka sallame su daga asibiti.
Ya yabawa al’ummar yankin bisa baiwa rundunar haɗin kai wajen magance aikata laifuka da fadan daga.