
Rundunar ƴansanda a jihar Jigawa ta ce ta kama wani matashi da ake zargi da sassara mahaifinsa har lahira.
Lamarin ya faru ne a safiyar yau Litinin a garin Sara da ke karamar hukumar Gwaram.
Tuni aka yi jana’izar mahaifin matashin – inda shi kuma yake tsare a wajen ƴansanda.
Mai magana da yawun ƴansanda jihar SP Lawan Shi’isu Adam, ya shaida wa BBC cewa jami’ansu sun tarar da mahaifin cikin jini lokacin da suka isa gidansa.
“Yaron ya sassare mahaifin nasa a kafaɗarsa, ya kuma yanka maƙogoronsa har zuwa kirjinsa. Nan da nan aka ɗauke shi zuwa asibiti a Birnin Kudu inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa,” in ji SP Lawan Shi’isu.
Ya ce an yi ƙoƙarin an kama matashin da kuma addar da ya yi amfani da ita wajen sare mahaifin nasa.
Kakakin ƴansandan ya ƙara da cewa yanzu suna yin bincike domin gano abin da ya sa matashin ya yi wa mahaifinsa irin wannan ɗanyen aiki.
“Matashin yana hannun mu a yanzu kuma muna ci gaba da bincike.