Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na’ura.

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta amince da kuskuren na’ura da ya kawo cikas ga sahihancin sakamakon jarabawar da aka yi ta bana a cibiyoyi 157 a fadin kasar nan.
Shugaban hukumar ta JAMB, Ishaq Oloyede, yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Laraba, ya ce sakamakon ɗalibai 379,997 abin ya shafa.
Ya ce hukumar ta gano matsalolin a cibiyar a Legas da Owerri, wanda hakan ya sa aka kasa dora amsoshin ɗaliban da abin ya shafa a kwanaki ukun farko na jarabawar.
Oloyede ya ce ba gano matsalar da daya daga cikin kamfanonin da ke bada na’urar yin jarrabawar ya haifar ba kafin a fitar da sakamakon.
Ya ce cibiyoyi 65 a Legas ɗalibai 206,610) da cibiyoyi 92 a shiyyar Owerri (ɗalibai 173,387) abin ya shafa, wanda ya kawo adadin wadanda abin ya shafa zuwa 379,997.