Monday, March 24
Shadow

2027: Hadakar Atiku da El-Rufai da Obi ba za ta iya kayar da APC ba — Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa babu wata haɗakar ‘yan siyasa da za ta iya sauke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Matsayar Shekarau na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, suka soki matsayar Gwamnatin Tarayya game da rikicin siyasa a Jihar Ribas a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja.

A wata sanarwa da Dr. Sule Yau ya fitar a madadin Shekarau, ya jaddada cewa, sabanin abin da wasu ke hasashe, wannan haɗaka kawai wata tarayya ce ta masu niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa, kuma babu wanda daga cikin jagororin wannan haɗaka da ya tuntubi shugabancin jam’iyyarsa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: 'Yan Shi'a sun koka kan cirewa matansu hijabi da 'yansanda suka yi a Abuja

Sanatan ya bayyana haɗakar a matsayin wata hadin guiwa ta wasu gungun mutane kawai, yana mai cewa, ko da suna da manyan sunaye, hakan ba ya nufin sun haɗe wuri guda domin zama jam’iyya guda ba.

A cewarsa, “Haɗakar wasu manyan jiga-jigai daga jam’iyyun adawa abu ne mai kyau, kamar yadda aka gani kwanan nan a ƙarƙashin abin da suke kira ‘coalition’ na jam’iyyun adawa.

“Babu ɗaya daga cikin manyan jagororin da ke tafe da shugabancin jam’iyyarsa. Kuma wannan taron wasu gungun mutane, duk da suna da manyan sunaye, ba za a kira shi ‘merger’ ba, domin a bisa doka, sai jam’iyyun da aka rijista ne kawai za su iya yin cikakken haɗaka.”

Karanta Wannan  Bidiyo: Yanda wannan matar ke lika hotunan budurwar mijinta akan titi ya dauki hankula

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *