
Tsohon Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya bayyana cewa a zamanin mulkinsa abubuwa sun tafi yanda ya kamata.
Ya bayyana hakane a gawarsa da wasu ‘yan jarida da suka kai masa ziyara a Daura.
Yace abubuwan ci gaba da ya kawo a zamanin mulkinsa za’a dade ana amfana dasu a Najeriya.
Shugaban ya bayyana cewa, a shekarar 2015 da ya karbi mulki, ya gaji matsaloli da yawa daga gwamnatin Jam’iyyar APC wanda suka hada dana rashin tsaro, matsalar tattalin arziki da sauransu.