Sunday, May 18
Shadow

Tsare-Tsarena sun sa farashin kayan abinci sun sauka fiye da kamin in hau mulki>>Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, farashin kayan abincin ya sauka saboda tsare-tsaren gwamnatinsa.

Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Daniel Bwala a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na AriseTV.

Ya kara da cewa, idan aka kwatanta yanda Najeriya take a yanzu da yanda take kamin shugaba Tinubu ya hau mulki za’a ga banbanci.

Ya koka da cewa kasafin kudin Najeriya duka bai wuce dala Biliyan $30 ba sannan ga asibitoci a lalace ga tituna a lalace da sauransu.

A karshe dai ya tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya sauka.

Karanta Wannan  Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *