Tuesday, March 18
Shadow

An kama mutane 2 da yiwa yarinya me shekaru 12 fyàd a jihar Yobe

‘Yansanda a jihar Yobe sun kama mutane 2 da ake zargin sun yiwa yarinya me shekaru 12 fyade a jihar.

Lamarin ya farune a kauyen Jalingo dake karamar hukumar Tarmuwa ta jihar.

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin a Damaturu ranar Litinin.

Ya kara da cewa lamarin ya farune ranar 15 ga watan Fabrairu da misalin karfe 3:30 na rana inda wanda ake zargin suka ja yarinyar zuwa daji suka zakke mata.

Ya kara da cewa, sun jiwa yarinyar ciwo inda aka kai ta Asibiti sannan kuma an kama wadanda ake zargin.

Karanta Wannan  Matsin Tattalin Arziki yayi yawa, 'Yan Najeriya ba zasu iya biya ba>>Majalisar Tarayya tacewa Ministan sadarwa maza a dakatar da karin kudin kiran waya da ake shirin yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *