
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Bindiga sun budewa motar matafiya kirar Sharon akan hanyar Sokoto zuwa Minna wuta i da suka kashe mutane biyu a cikin motar wasu kuma suka jikkata.
Lamarin ya farune a yayin da motar ta doshi mabiyar ‘yan Bindigar.
Rahoton daga kafar Zagazola Makama ya bayyana cewa, wanda aka kashe din mace da namiji ne.
An garzaya da gawarwakin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata zuwa Asibitin IBB Specialist Hospital dake Minna.