
Wani masanin kimiyya a kasar Ingila me suna Dr Jason Hodgson ya yi ikirarin cewa, mafi yawan mutane na da son aikata luwadi da madigo idan suka samu damar yin hakan.
Ya bayyanawa jaridar mailonline cewa duk da yake wadanda suka fito suka bayyana cewa su ‘yan Luwadi da madigo ne basu da yawa amma akwai masu irin wannan dabi’ar da yawa dake boyewa.
A cewarsa, idan wasu suka samu dama, suma zasu so aikata irin waccan masha’a.
Yana bayyana cewa, wannan dabi’a ce ta mafi yawan mutane tsakanin maza da mata wadda ke cewa bisexual watau mace tana son namiji sannan tana son mace ‘yar uwarta, hakanan namiji yana son mace amma kuma yana son namiji dan uwansa.
Saidai da yawa ko da a cikin Turawan sun karyata wannan masanin kimiyya inda suka ce kawai yana son yada badala ne kuma abinda ya fada karyane.
Kusan za’a iya yadda da hakan domin masu son yada luwadi da madigo suna ta kokarin watsashi a finafinai musaman na kasashen waje da sunan cewa wai ana nunawa masu irin wannan mummunar dabi’a kyama.