Friday, December 5
Shadow

Dalilin da yasa na kifar da gwamnatin Buhari duk da yake cewa nine shugaban ma’aikatansa>>IBB ya magantu

Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida,IBB ya bayyana dalilin da yasa ya kifar da Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari.

Ya bayyana hakane a littafinsa da ya wallafa wanda yayi bayani kan yanda ya gudanar da aikinsa.

IBB wanda shine shugaban ma’aikatan Gwamnatin Buhari a wancan lokacin yace bai gamsu da yanda Buhari ke gudanar da mulki ba shiyasa ya masa juyin mulki.

IBB yace tare suke mulki amma sam yaga tsare-tsaren Buhari basa kawo ci gaba a kasar shiyasa ya kifar dashi a shekarar 1985.

Karanta Wannan  Mun godewa Allah da kafuwar Jam'iyyar ADC, saboda ta fito mana da bakaken munafukan cikin jam'iyyar mu ta APC wanda suka Munafurci Tinubu a zaben 2023 Karara mun gansu>>Inji Ministan Sufurin Jiragen sama, Festus Keyamo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *