
Biyo bayan abinda Tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana na cewa, Juyin Mulkin da aka shrirya na shekarar 1966 ba na Inyamurai bane, Kungiyar kare muradin Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta nemi a biyata diyyar asarar da aka mata.
Kungiyar ta nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bata hakuri sannan a biyasu diyyar Naira Tiriliyan 10.
Kungiyar tace lamarin ya jefa Al’ummar Inyamurai cikin wahala wanda ta kai ga yakin Biafra.
Kungiyar tace an yi mata asara sosai inda aka kashe mata mutane miliyan 3 ciki hadda yara kanana da mata, kungiyar tace kuma har yanzu abin yana damun inyamurai.
Kungiyar tace dan haka suna neman shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a madadin gwamnatin data gabata, musamman ta Yakubu Gowon da ya basu hakuri kan lamarin.
Sun kara da cewa, kudin basu yi yawa ba, amma diyyace ta asarar da mutane kabilar Inyamurai suka tafka.