
Yan Nigeria Basu iya Tattali Ba Amma N8,000 zata iya canza rayuwar matashi Wanda yasan meya keyi – Inji Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima
DAGA Wakiliya ) Mataimakin shugaban ƙasa yace indai matashi zaiyi anfani dashi yadda ya dace, To Indai Allah yasamai arbarka cikin Shekara 1yr zai Tara abunda yafi karfi 100k.
Misali:
- Akwai kananun sana’a kamar su sana’ar Shoe Shiner, Saida Data, Saida Katin Waya, Saida Touch Light dadai sauransu, Wanda a maneji 8k zata ishi mutum ya fara, Kuma Idan Allah yasama Abun Arbarka, A Shekara ba karamun kudi zai Tara ba, Kenan 8k ta canza rayuwarsa, Ya kuma barranta daga Rokon mutane, Balle kuma 8k din ba sau daya za’aba mutum ba.
- Akwai iyayenmu mata a Gida da suke Dan Saida daddawa, Magi, Gullisuwa, Tuwon Madara dadai sauran kayan makwalashe Dana kayan miya, Kuma jarinsu yawanci bai wuce 8k ba, Amma kuma asirinsu a rufe basa roke-roke, To ya kuke gani idan aka basu 8k? Kenan In Sha Allah rayuwarsu zata iya canzawa.
Amma miye ra’ayinku?