
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, abuta tsakaninsa da Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ta kare.
Malam ya bayyana hakane ta shafinsa na Twitter inda wani yace Uba sanin ya watsar da mutanen da suka hana idanuwansu bacci dan ganin ya zama gwamna.
Saidai El-Rufai ya bayyana cewa, Kansa ya yaudara kuma ya rasa aboki.
Ko da a hirar da aka yi da El-Rufai a gidan talabijin na Arise TV ya bayyana cewa, Shi da Uba Sani da Nuhu Ribadu babu sauran abuta a tsakaninsu.