Sunday, March 16
Shadow

Sanata Natasha ta taba bani labari game da haduwarta da Sanata Akpabio a dakin Otal, saidai na mata gyara inda nace mata a ofis ake haduwa a yi aiki ba a otal ba>>Sanata Kingibe

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Sanata me wakiltar babban birnin tarayya, Abuja, Ireti Kingibe ta bayyana cewa, sanata Natasha Akpoti kamar diya take a wajenta saboda tazarar shekarun dake tsakaninsu.

Ta bayyana cewa a baya kamin dangantaka ta yi tsami tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Natasha, tafi kowace mace a majalisar samun damarmaki na ci gaba.

Tace kuma ba Sanata Natasha Akpoti kadai aka canjawa wajan zama ba.

Game da maganar zargin lalata da tawa Sanata Akpabio, sana Kingibe tace ita bata san komai ba akai.

Tace akwai dai sanda Sanata Natasha Akpoti bata zo wajan aiki ba, ta karbi takardu a madadinta dan ta kai mata gida.

Tace bayan data kawo mata abinci sai take ce mata zata gaya mata wata magana, wai Sanata Akpabio yace ta sameshi a dakin Otal.

Karanta Wannan  Gwamnatin Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti

Sanata Kingibe tace anan ta gayawa Sanata Akpoti cewa, ba’a aiki a dakin Otal, a Ofis ake haduwa ana aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *