
Kamfanin mai na kasa NNPCL, ya rage farashin litar mai daga naira 920, zuwa naira 860.
An samu wannan cigaba a daidai lokacin da ake samun gasa tsakanin manyan yan kasuwar mai dangane da farashin fetur, wanda a makon daya gabata matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man daga naira 890 zuwa naira 825.
Haka zalika hawa da saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya na taimakawa wajen samun hawa da saukar farashin.