Saturday, March 15
Shadow

Kotu a Kano ta ɗaure ƴan TikTok biyu kan wallafa bidiyo mai ɗauke da kalaman batsa

Wata kotun majistre da ke zama a anguwar Norman’s land a karamar hukumar Fagge a jihar Kano, ta ɗaure wasu ƴan TikTok biyu a gidan yari, bayan samunsu da laifin amfani da bidiyo mai ɗauke da kalaman batsa.

Hukumar tace fina-finai ta jihar ta kama mutanen ne Ahmad Isa da Maryam Musa mazauna anguwar Ladanai da ke Hotoro Quarters, inda daga bisani ta miƙa su ga kotun, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Lauyan gwamnatin jihar ta Kano, Barrister Garzali Maigari Bichi, ya same su da aikata laifi da ya kunshi haɗa baki don aikata laifi da kuma wallafa hotunan bidiyo masu ɗauke da kalaman batsa a shafukan sada zumunta.

Karanta Wannan  NAFDAC ta yi gargaɗi kan amfani da sinadarin Sniper don taskance abinci

Kotun ta ce bidiyon na rashin ɗa’a ya ci karo da addini da kuma tarbiyya a jihar ta Kano.

Mutanen biyu sun amsa aikata laifin.

Alkaliyar kotun, mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan ta yanke musu hukuncin zama gidan yari na shekara ɗaya ko kuma zaɓin biyan tarar naira 100,000 kowannensu – ta kuma hore su da su zama mutanen kirki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *