
‘Yan Jam’iyyar Republican dake mulki a kasar Amurka a majalisar kasar na shirin soke dokar amincewa da auren jinsi na ‘yan Luwadi da madigo a kasar.
A watan Janairu ne aka fara samun wanna kira daga ‘yan majalisar jihar Idaho inda suka nemi kotun kolin kasar data sake duba dokar da ta yi a shekarar 2015 data halasta auren jinsi.
Bayan su, an sake samun wasu ‘yan majalisar daga jihohin Michigan, Montana, North Dakota da South Dakota suma suna kiran kotun kolin data sake duba wannan hukunci nata.
Dama dai tun a ranar da aka bayyana cewa, Donald Trump ne ya lashe zaben shugaban kasar Amurka aka rika samun ‘yan Luwadi da madigo da yawa na kuka suna cewa sun shiga uku inda wasu suka bar kasar ta Amurka saboda sun san shugaban kasar, Donald Trump baya shiri dasu.
Tuni dai shugaba Trump ya haramta daukar wanda suka canja halittarsu daga mace zuwa Namiji ko daga Namiji zuwa mace aikin soja a kasar.