Sunday, March 23
Shadow

Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba>>Inji Dan Jarida Sam Omatseye

Dan Jarida, Sam Omatseye ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai so Tinubu ya zama ahugaban kasa ba.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.

Yace tun a shekarar farko aka so a samu matsala tsakanin Buhari da Tinubu amma saboda Buharin na tunanin zarcewa, shiyasa ba’a yi fadan ba.

Yace cire tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole daga mukamin shugaban APC na daya daga cikin dabarun hana Bola Ahmad Tinubu zama shugaban kasa da Gwamnatin Buhari ta bijiro dasu.

Yace hakanan akwai wasu gwamnoni ma da basu so Tinubu ya zama shugaban kasa ba.

Karanta Wannan  Ki kiyayi kanki ki janye zargin da kikewa dan mu in ba haka ba wallahi zamu durkusa mu gayawa Allah ya mana maganinki>>Matan Inyamurai dana Niger Delta suka gargadi Sanata Natasha Akpoti

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *