
Kotun daukaka kara dake Abuja ta yi dokar cewa bai kamata a hana masu rike da mukaman siyasa zuwa kasashen waje neman lafiya ba.
Kotun da Alkalai 3 suka jagoranci yin shari’ar sunce hana ‘yan siyasar zuwa kasar waje neman magani kamar take hakkinsu ne a matsayin ‘yan Adam.
Babban lauya me rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana ne ya shigar da wannan kara akan Gwamnatin tarayya.