
Wata Kungiyar matasan Inyamurai me suna COSEYL ta baiwa Fulani makiyaya awanni 48 su fice daga jihar Enugu.
A sanarwar da kungiyar ta fitar ta bakin shugabanta, Goodluck Ibem ta zargi makiyayan da yiwa mata fyade da kisa a wasu yankunan jihar.
Ya bayyana cewa ayyukan na Fulani makiyayan shedanci ne da mugunta inda yace suna Allah wadai da hakan.
Yace fulanin ‘yan ta’adda ne ba makiyaya ba yayi zargin cewa sunawa matansu fyade kuma su rika saka musu sanda a al’aurarsu.
Ya kara da cewa sun yi iya hakurin da zasu iyayi amma an kaisu bango.