
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Gwamnatinsa na kokarin ganin kowane gida a Najeriya ya samu wadataccen abinci me gina jiki.
Hakan ya fito ne daga Ministan Noma, Abubakar Kyari a yayin da yake kaddamar da shirin Noman Rani da rabon abincin watan Ramadana a jihar Kebbi.
Ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na kokarin samar da yanayi me kyau da kuma karfafa manoma dan su samar da amfani gona wadatacce da zai sa a samu wadatar abinci a kasarnan.
Yace Gwamnatin tarayya zata ci gaba da aiki da gwamnatocin jihohi dana kananan hukumomi dan ganin ta samar da ci gaba ta bangaren Noma.