Kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Kaduna ta kulle jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna Polytechnic biyo bayan yajin aikin data fara a yau, Litinin na sai baba ta gani.
NLC sun je reshen jami’ar dake Unguwan Rimi inda suka fitar da daliban dake ciki suka kulle makarantar, kamar yanda Channels TV ta ruwaito.
A Abuja ma dai haka lamarin yake inda NLC ta kulle guraren aiki da yawa ta hana ma’ikata shiga.