
Wata kungiyar Lauyoyi daga jihar Filato sun yi Allah wadai da hukumar ‘yansandan kan yanda suka nuna gawar tsohon shugaban hukumar Immigration da ya mutu a dakin otal bayan ganawa da wata mata.
Tsohon Kwamandan na hukumar Immigration David Parradang da farko an ruwaito cewa an yi garkuwa dashi ne, saidai daga baya an musanta wannan ikirarin.
Hukumar ‘yansandan Najeriya a ranar 4 ga watan Maris sun bayyana cewa, ya mutu ne a dakin otal bayan ganawa da wata mata.
Da take mayar da martani kan lamarin, kungiyar Lauyoyin daga jihar Filato, The PLBF ta bayyana cewa, nuna hoton gawar David cin fuska ne wanda bai kamata ba.
Ta kara da cewa yada labarin da bai inganta ba akan David din bata masa sunane
Hakanan kungiyar Lauyoyin ta bayyana cewa, shiruj da hukumar Immigration ta yi akan lamarin bai dace ba.