
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yaran da ba’a haifa nan gaba bane yake son ya baiwa kariya shiyasa ya cirw tallafin man fetur.
Shugaban ya bayyana hakane a fadarsa wajan kaddamar da kwamitin ci gaban matasa inda yace gwamnatinsa zata ci gaba da baiwa matasa kwarin gwiwa.
Shugaban yace idan ka duba masu karfafa cewa a bar Najeriya a tafi wata kasa ci rani, saboda babu ci gaba sosai, amma idan aka samu ci gaba, babu wanda zai so ya tafi wata kasar.
Shugaban yace a lokaci da ya fara mulki, matsaloli sun yi yawa inda ake ta kuka, yace amma yanzu tattalin arziki ya fara farfadowa inda farashin kayan masarufi ya sauka.