Wednesday, March 19
Shadow

Ji labarin Ushie Uguamaye, ‘Yar bautar kasa data tayarwa da gwamnatin Tarayya hankali saboda sukar Gwamnatin Tinubu, Saidai Atiku, da Peter Obi sun goyi bayanta

Ƴan Najeriya na ta musayar yawu dangane da makomar Ushie Uguamaye mai yi wa ƙasa hidima mazauniyar birnin Legas, tun bayan da ta yi zargin fuskantar barazana sakamakon kalamanta da ta yi a shafinta na tiktok inda ta soki gwamnatin Bola Tinubu.

Tuni dai jagororin adawa na Najeriya da kuma ƙungiyoyi masu rajin kare haƙƙin bil’adama suka nemi da hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta tabbatar da cewa babu abin da ya samu Ushie Uguamaye.

Ita dai hukumar ta NYSC ba ta ce uffan ba dangane da zargin barazanar da Ushie Uguamaye ta yi.

Me Ushie Uguamaye ta faɗi?

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na tiktok ranar Asabar, Ushie Rita Uguamaye ta bayyana damuwa kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi a Najeriya inda ta nuna takaicinta kan yadda jajircewa ke neman zama aikin banza.

Ta kuma fito fili ta soki gwamnatin Bola Tinubu inda ta bayyana shi da “mugun shugaba,” sannan ta kuma ta dasa ayar tambaya kan shirin gwamnatin na yayewa ƴan ƙasar talaucin da ke damun su.

Har wa yau, ƴar bautar ƙasar da ke zaune a birnin Legas, ta bayyana birnin da “jiha mai wari” tana mai ƙorafi da gurɓacewar iska da cunkoson da jihar ke fuskanta.

Karanta Wannan  Kamfanonin sadarwa sun yi barazanar mayar da sabis karɓa-karɓa

To sai dai kuma jim kaɗan bayan bidiyon nata, sai ta sake fitar da wani inda take bayyana cewa tana fuskantar barazana daga hukumar yi wa ƙasa hidima bisa kalaman nata.

“Ya ku ƴan uwana ƴan Najeriya, sun saurari bayanina. Idan ba ku ƙara jin ɗuriyata ba a intanet , kun san wa za ku kama da laifi. Ban yi wani abun da ba daidai ba kawai dai na nemi da su yi wani abu kan hauhawar farashi.”

Me zai hana ni yin magana? Kasancewar mutum mai yi wa ƙasa hidima bai ba ya nufin na sarayar da ƴancina na yin ƙorafi.” In ji Ushie Rita Uguamaye.

Ushie Uguamaye ƴar gwagwarmaya ce – Atiku

Atiku Abubakar ya ce ƴar NYSC wadda ake zargi da sukar shugaban Najeriya, Bola Tinubu ta kama hanyar zama ƴar gwagwarmaya ce.

Atiku ya bayyana haka a shafukansa na sadarwa, inda ya ce, “rashin tsoronta da hikimarta sun birge ni, musamman yadda ta iya bayyana gaskiyarta game da masu mulki ba tare da tsoro ba.

Karanta Wannan  An zargi mutane 64 da yi wa wata matashiya fyaɗe a India

“Ta ɗauki tafarkin mata ƴan gwagwarmaya irin su Gambo Sawaba da Funmilayo Ransom-Kuti da Margaret Ekpo da ire-irensu ne.

Ya ce matashiyar ta cancanci goyon baya da ƙarfafa gwiwa ne, “saboda ta zama wata fitilla a tsakanin matasan Najeriya, wanda hakan ke nuna lallai akwai shugabannin gobe a cikin matasanmu da suke jiran dama.”

Ni ma ina fuskantar abin da Ushie ke fuskanta – Peter Obi

Shi ma ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar LP, Peter Obi ya ce yana goyon bayan Rita domin ba ta aikata wani laifi ba.

“Rahotanni na nuna cewa Rita ta fuskanci barazana daga NYSC saboda ta bayyana ra’ayinta kan halin da ake ciki.

Ba ita kaɗai take fuskantar irin wannan barazanar ba. Ni ma ina fuskanta saboda ƙoƙarina na bayar da shawarwari masu ma’ana na yadda za a tafiyar da ƙasa.

Ina kira ga ƴan Najeriya da ka da su bari a rufe bakunansu wajen faɗar albarkacin bakinsu sannan ina kira ga gwamnati da ta karɓi ƙorafe-ƙorafen ƴan ƙasa a matsayin hanyar gyara.” In ji Peter Obi.

Karanta Wannan  Kai ba karamin yaro bane, ya kamata ka sawa Zuciyarka dangana akan maganar rasa mukamin Minista>>Tinubu ya gayawa El-Rufai

Ushie ba ta yi laifi ba – Amnesty International

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International Nigeria ta yi kakkausan suka dangane da barazanar da ake yi wa Ushie Uguamaye inda ƙungiyar ta ce ƴar bautar ƙasar na da ƴancin faɗin albarkacin baki.

A wani bayani da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, Amnesty ta ce ta samu labarin zargin barazanar da ake yi wa ƴar bautar ƙasar daga hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, inda ta ƙara da cewa Uguamaye ba ta yi laifi ba domin ta aikata wani ɓangare ne na ƴancin da kundin mulki ya bata.

A wata tattaunawa da BBC, shugaban ƙungiyar, Malam Isa Sanusi ya shaida cewa:

“Ya kamata gwamnatin Najeriya ta sani cewa wannan yarinyar ba ta yi laifi ba ko kaɗan sannan ya kamata ƴan gwamnatin su sani cewa idan ban da ƴacin faɗin albarkacin baki to da yanzu mafi yawancinsu suna kurkuku ne.” In ji Isa Sanusi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *