Saturday, June 27
Shadow

A kudancin Kaduna, Gwamnatin mu ta APC bata tabuka abin Arziki ba>>Inji Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Gwamnatinsu ta APC bata tabuka abin a zo a gani ba a kudancin jihar kaduna.

Ya bayyana hakane a matsayin suka ga gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.

El-Rufai ya shafe shekaru 8 yana a matsayin gwamnan Kaduna saidai a kwanannan ya bar jam’iyyar APC zuwa PDP.

A ci gaba da bayaninsa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Amma gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta canja akalar yankin inda ta kawo mai ci gaba.

Ya bayar da misali na ci gaban da gwamnatin Tinubu ta kai yankin kudancin jihar Kaduna inda yace kwanannan Shugaba Tinubun ya sakawa kudirin dokar samar da jami’ar kimiyya da fasaha ta Federal University of Applied Sciences hannu wadda za’a bude a karamar hukumar Kachia.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Gwamnati na shirin kara farashin man fetur zuwa Naira 1,405 dan tatsar kudaden da zata biya bashin da 'yan kasuwar man fetur ke binta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *