Monday, December 16
Shadow

Mexico ta zaɓi mace ta farko shugabar ƙasa

An zabi Claudia Sheinbaum a matsayin shugabar ƙasa mace ta farko a Mexico bayan gagarumar nasara da ta yi a zaɓen da aka gudanar a jiya Lahadi.

Hukumar zaɓen ƙasar ta Mexico ta ce sakamakon farko da aka gudanar ya nuna tsohuwar shugabar birnin Mexico City ƴar shekara 61 ta samu tsakanin kashi 58 da kashi 60 na kuri’un da aka kaɗa a zaben.

Hakan ya ba ta jagorar kusan kashi 30 cikin 100 a kan babbar abokiyar hamayyarta, ‘yar kasuwa Xóchitl Gálvez.

Ms Sheinbaum za ta maye gurbin jigonta a siyasa, shugaba mai barin gado Andrés Manuel López Obrador, a ranar 1 ga Oktoba, na wannan shekara.

Karanta Wannan  Idan aka biya ma'aikata mafi karancin Albashin da suke nema na Naira N494,000 sauran mutanen Najeriya zasu shiga wahala>>Ministan Yada Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *