Sunday, May 18
Shadow

A watan Maris matasa masu bautar kasa zasu fara karbar Alawus din Naira dubu 77>>Inji NYSC DG

Hukumar kula da masu bautar kasa a Najeriya, NYSC ta baiwa matasa masu bautar kasar tabbacin cewa, a watan Maris zasu fara ganin karin Alawus zuwa Naira 77,000.

Shugaban hukumar, Brigadier General Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da matasan masu bautar kasa a ranar Alhamis.

An yi taron ganawar ne a Wuse da Garki a Abuja.

Brigadier General Nafiu ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin tarayya da Hukumar ta NYSC na kokarin ganin sun jiyawa matasan masu bautar kasa dadi.

Karanta Wannan  Bidiyo: Ya kamata a bar mutanen Najeriya su rike màkàmài dan baiwa kansu kariya>>Ado Doguwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *