
Kasar Burkina Faso ta dakatar da shigar mata da kayan Gwanjo daga kasar Amurka.
Gwamnatin Mulkin Soji ta shugaban kasar, Ibrahim Traore ce ta bayyana hakan.
Ko da a baya ma dai Gwamnatin ta hana Kasar Saudiyya gina mata masallatai inda tace maimakon haka a gina mata masana’antu.
Shugaba Ibrahim dai na ta kawo sauyi a gwamnatin kasar tun bayan da ya hau mulki.