Tuesday, April 29
Shadow

Mijinane baya kulani:Inji Wannan malamar da aka kama tana lalatawa dalibinta tarbiyya ta hanyar aika masa hotunan Batsà da yin lalata dashi

Wannan malamar makarantar me suna Emily Nutley an kamata tana lalatawa dalibinta tarbiyya ta hanyar tura masa hotunan batsa da yin lalata dashi.

Malamar dai na aikin koyarwa ne a makarantar St. Xavier High School dake garin Cincinnati na jihar Ohio.

An sakata ta rika kula da dalibai wanda basu da kokari sosai da makinsu bai da yawa.

Inda a nan ne ta hadu da dalibin me shekaru 17. Ta fara aika masa sakonnin soyayya da hotunan batsa bayan an tashi daga karatu inda daga karshe dai har ta kai ga sun yi lalata.

Dalibin dai a karshe ya nemi su daina abinda suke amma ta kiya.

Karanta Wannan  Mutane a jihar Sokoto sun biya 'yan Bindiga Naira Biliyan 160 a matsayin kudin fansa

A karshe dai an kamata inda ta amsa laifinta.

Rahotanni daga kafar Fox19 NOW sun ce zata iya fuskantar daurin shekaru 10 a gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *