
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayse ya bayyana cewa, a zaben shekarar 2023 ya yiwa Atiku Abubakar makarkashiya.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels.
Yace babbar matsalar da aka samu a PDP shine da aka baiwa dan Arewa damar tsayawa takarar shugaban kasa bayan da dan Arewa ya kammala shekaru 8 yana mulki.
Yace Najeriya tafi PDP muhimmanci.
Yace kuma idan Atiku ya sake cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027, zai sake yi masa makarkashiya.
Hakan ya zowa mutane da yawa da bazata musamman ganin cewa, shi Fayose dan PDP ne.