Monday, May 19
Shadow

Ina mamaki idan naga ‘yan Siyasa na turuwa zuwa gidan Buhari, Buhari yawa ‘yan Najeriya yaudarara da ba’a taba musu irinta ba>>Inji Buba Galadima

Tsohon na hannun damar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya bayyana Buhari a matsayin wanda yawa ‘yan Najeriya yaudarar da ba’a taba musu irin ta ba.

Ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punchng ta yi dashi.

Yace ya yiwa Buhari yakin neman zabe a baya kuma dashi aka kafa jam’iyyar APC amma maganar gaskiya Buhari ya boye bakar aniyarsa ce a zuciya inda ya rika nuna yana tare da talakawa, sai daya hau mulki ya fito da ainahin kalarsa.

Yace amma ba zai yi magana sosai akan lamarin ba ‘yan Najeriya ne zasuwa kansu alkalanci game da wanene Buhari.

Ya kara da cewa Buhari kamata yayi ya koma ya ci gaba da neman gafarar Allah biyo bayan zaluncin da yawa mutane.

Karanta Wannan  MASHA ALLAH: Maryam Kenechi Kenan, Ƴar Ķabilar Ibo Da Ta Karɓi Mùśùluñci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *