Saturday, December 13
Shadow

Kalli Hoto: Yanda aka kama sojan Najeriya, Yahya Yunusa na safarar makamai a Kaduna

An kama karamin sojan Najeriya me suna Private Yahaya Yunusa a Jaji dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna saboda zargin safarar makamai.

Sojan dake aiki a bataliya ta 197 dake jihar Zamfara an kamashine ranar Juma’a da misalin karfe 11:55 a.m. inda aka samu albarusai 214 a wajensa.

An kuma kamashi da ATM da yawa.

Ya amsa laifinsa inda yace ya saci albarusanne daga wajen aikinsa dan shine ke kula da bindigar A.A da ake kafewa a bayan motar yakin sojoji.

Karanta Wannan  Wai wa ke baiwa Sheikh Dr. Ahmad Gumi kariyane a Najeriya an kasa hukuntashi kan abubuwan da ya aikata da basu kamata ba? Baturen kasar Ingila, Deacon Nick Donnelly ya tambaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *