Likitocin jihar Yobe karkashin kungiyarsu ta (NMA) basu shiga yajin aikin kungiyar kwadago ta NLC ba a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar na jihar, Dr Abubakar Kawu Mai Mala ne ya bayyana hakan inda yace duk da yake ‘yan uwa ne su da NLC amma basa karkashin kungiyar.
Ya kara da cewa, kuma bangaren lafiya a jihar ta Yobe na da matukar muhimmancin da baza’a kulleshi ba gaba daya.