Sufeto Janar na Ƴansanda, Dr. Kayode Egbetokun, ya shawarci al’ummomin da jami’an tsaro ke aiki a yankunan su da su daina ba su rancen manyan kudade waɗanda za su wahala wajen biya.

IG ɗin, wanda Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kogi, Miller Dantawaye, ya wakilta, ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin bikin ƙaddamar da sabuwar hedikwatar ‘yansanda a gundumar Imane, karamar hukumar Olamaboro ta jihar.
“Bari in ja kunnen al’ummar yankin cewa yayin da suke mu’amala da jami’an da za a turo musu, wasu daga cikinsu za su nemi taimakon kuɗi da rance, amma kada ku ba su rance mai yawa da za su gagara biya,” in ji Dantawaye.
Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su kula da sabon ofishin ‘yan sanda, wanda shine irinsa na farko a yankin, wanda wani ɗan asalin yankin, Dr. Peter Ali, ya gina kuma ya bayar kyauta.
Haka kuma, Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, wanda Mataimakinsa, Joel Oyibo, ya wakilta, ya nuna godiyar gwamnatin jihar ga kyautar da aka bayar, sannan ya ƙarfafa al’umma da su haɗa kai da jami’an da za a turo don yin aiki a yankin.