Friday, December 5
Shadow

Hukumomin kasar Amurka sun nemi a kara musu kwanaki 10 kamin su fitar da bayanan zargin safarar miyagun Kwàyòyì da akewa shugaban Tinubu

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, Hukumar tsaro ta FBI da masu kula da harkar kwayoyi sun nemi a kara musu kwanaki 90 kamin su fitar da bayanai kan shari’ar zargin da akewa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ta Safarar Kwayoyi.

Ana zargin a shekarar 1990 ne dai Shugaba Tinubu da wasu mutane 3 Lee Andrew Edwards, Mueez Abegboyega Akande, da Abiodun Agbele suka yi safarar kwayoyi a birnin Chicago na kasar.

Wani lauya a kasar Amurka, Aaron Greenspan ne ya nemi wadannan bayanai.

Kuma kotu ta nemi hukumomin FBI da DEA su fitar da bayanan inda aka saka ranar 2 ga watan Mayu dan fitar dasu.

Karanta Wannan  Sanatan Kasar Amurka da ya zuga Donald Trump ya kawowa Najeriya Khari yace kwanannan zasu bayyana sunayen masu goyon bayan Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya

Saidai yayin da ake dakon jiran wadannan bayanai, wadannan hukumomin sun bayyana cewa basu kammalu ba sai nan da kwanaki 90.

Saidai Lauyan Aaron Greenspan ya bayyana cewa, kwanaki 90 sun yi yawa inda ya nemi a karawa FBI da DEA kwanki 14 kacal musamman kasancewar suna ta jan kafa wajan kin amincewa su saki bayanan game da shugaba Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *