Gwamnan jihar Rivers, Sim Fubara ya baiwa mahajjatan jiharsa kyautar dala $300.
Ya bukata mahajjatan da su zama wakilan jihar da kuma Najeriya na gari a kasa me.tsarki, kada su yi abinda zai bata sunan jihar ko Najeriya.
Ya kuma bakaci mahajjatan da su saka Najeriya a addu’a a yayin ibadarsu a kasa me tsarki.