Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, matakan tada komadar tattalin arziki da zata dauka nan gaba, sai sun fi na baya tsanani.
Hakan na fitowane daga bakin Ministan yada labarai, Muhammad Idris.
Ya kara da cewa daukar wadannan matakai ya zama dole dan canja fasalin Najeriya ta yanda zata ci gaba ta fannin tattalin arziki.
Ya bayyana hakane a wani rahoto da aka wallafa a wata jaridar kasar Ingila.
Minista Muhammad Idris ya kara da cewa, Shugaba Tinubu gwarzo ne dan kuwa ya dauki matakan da shuwagabannin da suka gabata, suka kasa daukar irinsu.
Babban matakin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta dauka wanda ya damu al’ummar kasar shine cire tallafin man fetur wanda ya yi sanadiyyar jefa mutane cikin halin kaka nikayi.
Hakanan gwamnatin Tinubun ta kuma cire tallafin man dala da sauransu, matakan da masana da yawa ke cewa aun yi tsauri.
Ga dai abinda ministan ya fada kamar haka:
““More difficult decisions lie ahead before Nigeria is reshaped and growing economically to the benefit of its citizens and the wider continent of Africa. The administration has joined the Global Methane Pledge, intended to reduce emissions from our oil industry.“
[…] Ko da a jiya, saida Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, zata sake daukar matakai masu tsauri wan… […]