Friday, December 12
Shadow

Har yanzu akwai masu yiwa matatar man fetur dina makarkashiya>>Inji Dangote

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, har yanzu akwai masu yiwa matatar mansa makarkashiya, Dangote ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai.

Dangote yace mutanen da suka yaki cire tallafin man fetur ma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne suke yaki dashi dan ganin matatar man sa bata yi nasara ba.

Saidai Dangote yace dama ya saba da irin wannan kalubale kuma yasan zai yi nasara.

Kafar yada labarai ta Semafor ce ta ruwaito hakan bayan tattaunawa da Dangote a wajan wani taron masu zuba hannun jari a Legas.

Karanta Wannan  Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi karin haske kan maganar komawarsa PDP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *