
Wani sabon rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna yadda talauci ƙaruwa a yankunan karkara a Najeriya, inda alaƙluma ke nuna ya ƙaru zuwa kashi 75 cikin 100 a watan Afrilu.
Rahoton da bankin ya fitar na watan Afrlun 2025, ya nuna cewa talaucin dai ya ƙaru a ɓangren karkara idan aka kwatanta da yadda yake a biranen ƙasar.
Rahoton ya yi nazari kan girman talauci a ƙasashen duniya, yana mai bayyana kashi 30.9 cikin 100 na ‘yan Najeriya na rayuwa ne kasa da dala biyu a kowacce rana a shekara ta 2018/2019 – kafin annobar korona.
Haka kuma, rahoton ya nuna cewar ‘wasu alkaluma da aka fitar na 2018/2019 ya nuna cewar akwai karin mutum miliyan 42 da suka sake faɗawa cikin talauci a Najeriya, wanda hakan ke nuni da fiye da rabin al’ummar ƙasar wato kashi 54% da aka yi ƙiyasin na fama da talauci a shekara ta 2024.
Alƙaluman sun kuma nuna cewar yara daga shekaru 1 zuwa 14 na daga cikin wadanda talaucin zai fi tasiri a kansu idan alƙaluman suka kai 72.5%.
Sannan ya nuna cewar kashi 63.9% daga mata da kashi 63.1 na maza da ke rukunin talauci a tsakanin masu matsakaicin karfi, na fadawa talaucin da zai sa su dinga rayuwa cikin ƙasa da dala $3.65 a kowace rana.
Sai dai rahoton ya nuna cewar kafin a samu annobar korona, an samu jinkiri wajen samun raguwar talauci a Najeriya. “An samu matuƙar jinkiri wajen rage kaifin talauci a Najeriya, wanda ya ragu da kasa da kashi 1 cikin 100 tun 2010,” a cewar bakin.
Bankin duniyar ya kuma nuna yadda kashi 32% na ƴan Najeriya ba su samun ruwan sha mai tsafta, sannan kashi 45.1% ba su rayuwa a muhalli mai cikakkiyar tsafta. Kashi 39.4% ba su samun wutar lantarki. Sannan kashi 17.6% na manya ba su kammala makarantar firaimare ba, yayin da kuma kashi 9% a cikin kowane gidaje akwai yaran da ba su zuwa makaranta.
Abubuwan da suka janyo ƙaruwar talaucin
Wasu daga cikin dalilan da babban bankin duniyar ya bayar a cikin rahoton nasa da suka haifar da ƙaruwar talaucin a Najeriya musamman a karkara sun haɗa da:
- Raunin tsarin tattalin arzikin da ƙasar ta jima da ginuwa a kai
- Dogaro da man fetur tsawon lokaci wajen bunƙasa tattalin arziki
- Matsalolin tsaro
- Rashin samar da aikin yi ga ƴan ƙasar
- Rashin bunƙasa harkokin noma, musamman a yankunan karkara
- Ƙarancin bunkasa a ɓangaren Ilimi
- Tashin farashin man fetur
Bankin duniya ya nuna cewa mutane a karkara sun dogara ne da aikn noma, sai dai suna fama da ƙarancin kayan bunkasa noman da zai tafi daidai da zamani, wanda shi ma ya ƙara taimakawa wajen haifar da ƙaruwa a sauyin yanayi da ake fama da shi a kasar.
“Akwai bukatar hukumomin Najeriya su tabbatar da sauya akalar tattalin arzikinta, ta hanyar rage dogaro da man fetur zuwa ɓangarorin da za su bunkasa zuba jari a ɓanagrorin da za su bunƙasa rayuwar ƴan kasar,” in ji bankin.
‘Ya kamata gwamnati ta sauya shawara’
Sai dai masana tattalin arziki a Najeriya na cewar akwai buƙatar gwamantin ƙasar ta fara watsi da wasu daga cikin ƙa’idoji ko shawarwari da bankin duniyar ke ba ta idan har ta na son magance ƙaruwar talaucin da ake fuskanta a ƙauyukan kasar, da ma birane.
Farfesa Muntaƙa Usman na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya ce sun yi wannan hasashe tsawon shekaru uku da suka gabata na cewar idan ba a suya salon yadda ake tafi da harkoin tattalin arzika a kasar ba, fatara da giɓin da ke tsakin mai shi da mara shi zai ƙara yawa.
“Mutanen da ke ba ku shawarar na faɗa muku abin da suke so ku yi, sannan kuna yinsu amma tattalin arzikinku na ƙara taɓarɓarewa,” in ji shi.
“To ya kamata a tsaya a yi nazari domin gano waɗanne shawarwarin da ake ba mu ne suke haifar mana da wannan matsalar?
“Akwai buƙatar lallai gwamnatin Najeriya ta yi watsi da irin shawarwarin da Bankin Duniya da IMF ke ba ta, musamman wadanda ke janyo ƙaruwar talauci ga al’ummar ta.”
Rahoton na Bankin Duniya dai ya ce duk da cewar hukumomi a Najeiryar sun samar da wasu daga cikin hanyoyi da suke tunanin ka iya daƙile karuwar talauci, musamman shirin nan na bayar da tallafin kuɗi ga yan kasa na korona na fitar da gidaje miliyan 15 daga talauci, shirin bai yi tasirin da ake bukata ba.
Farfesa Muntaka ya ce akwai wasu matakai da idan gwamantocin na Najeriya suka dauka za a iya samun mafita tare da rage ƙaruwar talaucin a tsakanin al’ummar kasar.
“Idan Najeriya na son shawo kan waɗannan matsaloli bayan yi wa shawarwarin da bankin duniyar da IMF ke ba ta, sai ta bunkasa bangaren Ilimi, da na lafiya, da samar da abubwan more rayuwa, da inganta harkokin tsaro, da yadda mutane za su samu sauƙin sufurin da za su iya fita gudanar da harkokinsu na yau da kullum”, In ji Farfesa Muntaƙa Usman.
Wannan dai na zuwa ne bayan da wani rahoto da Bankin Duniyar ya gabatar a yayin taron bazara na aususn IMF da Bankin Duniya da aka gudanar a Washington DC, inda bankin ya yi hasashen cewa za a samu ƙarin miliyoyin ƴan Najeriya da za su auka cikin talauci nan da shekarar 2027 yana mai cewa talauci zai ƙaru da kashi 3.6 cikin 100.