Friday, December 5
Shadow

‘Yan Bìndìgà sun kàshè soja me mukamin Kyaftin da wani soja daya a Borno

”Yan Bindiga da ake kyautata zaton mayakan Bòkò Hàràm ne sun kashe soja me mukamin Kyaftin a garin Izge na karamar hukumar Gwoza ta jihar.

Lamarin ya farune da safiyar ranar Laraba da misalin karfe 1 na dare.

Hakanan aun kuma kashe soja daya.

Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta ya tabbatar da faruwar lamarin.

Saidai sojojin da ‘yan Bijilante da mutanen Gari sun yiwa ‘yan Bòkò Hàràm din Rubdugu inda suka kashe 3 daga ciki, sauran suka tsere suka bar makamansu da Mashina 10.

Sojoji dai na bin sahun wanda suka tsere.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ku Jahilai Masu cewa wai ni mawakine in daina saka baki wajan kare Annabi, ku je ku tambayi malamanku irin gudummawar da mawaka suka bayar wajan kare Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Tijjani Gandu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *