Friday, December 5
Shadow

Mijina ba zai sake neman takarar shugaban kasa ba, Tinubu zamuwa Yakin neman zabe saboda aikinsa na kyau>>Inji Matar tsohon shugaban kasa, Patient Jonathan

Matar tsohon shugaban kasa, Dame Patient Jonathan ta bayyana cewa, Mijinta ba zai nemi takarar shugaban kasa ba.

Ta bayyana cewa, Maimakon haka, zata hada kai da matar shugaban kasa, Remi Tinubu dan su yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yakin neman zabe.

Ta bayyana hakane a yayin wata kyautar karramawa da aka bata a Abuja.

Tace a baya lokacin da mijinta ya fito takarar shugaban kasa a 2011 Itama Remi Tinubu da mijinta shugaban kasa sun taimaka musu.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Sanata Natasha Akpoti ta bani Naira Miliyan 200 dan in kalawa Sanata Godswill Akpabio sharri>>Inji Dr. Duru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *