Thursday, November 5
Shadow

Gwamnatin tarayya ta bayyana ainahin wanda zasu amfana da tallafin Dubu hamsin da take bayarwa

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ainahin wadanda zasu iya amfana da tallafin Naira Dubu hamsin da take bayarwa.

Ministan jin kai da kawar da talauci, Dr Bernard Doro ne ya bayyana hakan.

Yace na farko dai matakan da suke bi wajan tantance wadanda ya kamata su samu wannan tallafi shine.

Suna tabbatar da mutum nada lambar katin dan kasa, NIN.

Sannan yace suna tabbatar da cewa, Mutum na cikin rijistar talakawan Najeriya masu bukatar taimako.

Rijistar Talakawan Najeriya na dauke da mutane Miliyan 70 dake cikin matsanancin Talauci.

Wadanda yawanci an samosu ne daga kananan Hukumomin dake fadin Najeriya.

Karanta Wannan  Karamin yaro dan shekaru 4 ya kkàshè kansa ta hanyar hàrbìn kansa da Bìndìgàr iyayensa da yake wasa da ita a cikin mota

Ministan ya kara da cewa, Tallafin kyautane ba sai mutum ya bayar da komai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *