
Rahotanni sun bayyana cewa, babbar Kotun tarayya ta soke takarar shugaban kasa ta Alhaji Atiku Abubakar.
Kotun ta soke takarar ne bayan karar da Nafiu Bala ya shigar a gabanta yake kalunalantar Shugabancin David Mark da ayyukan da yayi.
Nafiu Bala yace bayan saukar shugaban jam’iyyar, shine halastaccen shugaban da ya kamata ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar ADC.
Sannan kuma ya nemi a soke takarar shugaban kasa ta Atiku Abubakar.
Alkalin kotun Peter Lifu ya amince da duka bukatun Nafiu Bala.
Saidai bangaren jam’iyyar ADC din bangarw su Atiku sun ce zasu daukaka kara.