Majalisar Dinkin Duniya ta saka kasar Israela cikin kasashe masu kisan kananan yara.
Hakan ya biyo bayan kisan sa kasar kewa Falas-dinawa a zirin gaza.
Wakilin Israela a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan ne ya bayyana haka. Inda yace an sanar dashi matakinne ranar Juma’a.
Hakanan ministan harkokin kasashen waje na kasar Israela, Katz ya bayyana cewa, zasu dauki mataki kuma wannan abu da majalisar ta yi zai canja dangantakar dake tsakaninsu da Israela.