Mun Gama Ýanke Shawarar Mayar Da Tinubu Jihar Legas A Zaben 2027, Domin Za Mu Dakatar Da Shi Daga Zarcewa A Mulki Karo Na Biyu, Inji El-Rufai.

Daga Comr Nura Siniya
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa akwai wani muhimmin yunkuri na kafa hadaka da nufin ganin an dakatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga sake samun mulki a karo na biyu.
Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin taron baje kolin fasaha da ƙirƙira na “Arewa TechFest da aka gudanar a jihar Katsina ranar Laraba 21 ga watan Mayu 2025.
A cewarsa, “Jiya da karfe 8 na dare, mun gudanar da wani muhimmin taro na hadakar da muke kokarin kafa wa domin tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya koma Legas.”
Duk da wannan yunkuri, El-Rufai ya jaddada cewa akwai ministocin da suke ganin sun cancanci ci gaba da aiki, inda ya ambaci Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani, Bosun Tijani, a matsayin daya daga cikinsu. “Mun yanke shawarar cewa za mu ci gaba da rike Bosun Tijani, za mu barshi a matsayin minista domin yana yin aiki mai kyau,” in ji shi.
Wannan jawabi ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman duba da irin rawar da El-Rufai ke takawa a harkokin siyasar Najeriya da kuma yadda yake tasiri a shiyyar Arewa.
Taron Arewa TechFest dai wani babban taro ne da ke hada matasa, masana kimiyya, da ‘yan kasuwa domin karfafa bangaren fasahar zamani a Arewacin Najeriya.
Sai dai El-Rufai ya yabi ministan matasa na Tinubu Basoum Tijjani inda yace yana ƙoƙari za su bar shi kan mukaminsa idan har suka maida Tinubu Lagos.
Ya kuke kallon wannan batu?