Friday, December 5
Shadow

Hankula sun tashi bayan da aka dauke wutar lantarki a kasar Faransa na tsawon awanni 5

Rahotanni daga birnin Riviera na kasar Faransa inda ake bikin fina-finai na kasa da kasa na cewa, an dauke wuta na tsawon akalla awanni 5.

Hakan ya kawo tarnaki a bikin finafinan da ake yi inda baki da dama da suka je wajan bikin ke kokawa musamman game da maganar kudi da zasu yi hidima dasu saboda bankuna da ATM duk sun samu tangarda saboda rashin wutar.

Rahotanni sun ce wasu bata garine suka lalata kadarorin wutar lantarkin wanda hakan ya kawo tarnaki aka dauke wutar.

Lamarin ya zowa mutane da mamaki ganin kasa me ci gaba irin Faransa ta samu matsalar wutar lantarki haka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Bansan Iya mazan da suka yi lalata dani ba bayan da mijina ya sakeni>>Inji Wannan Bazawarar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *